<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>2</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ubanginmu, Mai Ceto,
 Don zumunta ne muka zo.
 A duniyan nan sai sakewa,
 Wurinka fa sai hutawa.

[V2]
 2) Tun jiya, yau, har abada,
 Madauwami ne sunanka!
 Kai ne ka kafa duniyan nan,
 Kai ne mai shirya gida can.

[V3]
 3) Almasihu, Cetonmu,
 Ba mu da wani taimako,
 Amma ƙaunarka cikakkiya,
 Ita ce garkuwar ƴaƴanka.

[V4]
 4) Ƙaunarka ! har wa yau ta tsaya
 Da, ka ɗanɗana mutuwa.
 Can bisa kursiyin Allahnmu,
 Yanzu ka rayu dominmu.

[V5]
 5) Yabo, daraja, godiya
 Gare ka Yesu Ɗan Allah!
 Ka cika mu da Ruhunka,
 Ya koya mana nufinka.</lyrics>
<title>Ubanginmu, Mai Ceto LW2</title>
</song>